Bafarawa da Wamakko sun kaure da wani gajeren rikici a filin jirgin Sultan Abubakar III.

Legit Hausa

Mun samu labari cewa tsofaffin gwamnonin jihar Sokoto biyu, Attahiru
Dalhatu Bafarawa da Aliyu Magatakarda Wamakko sun kaure da wani
gajeren rikici a filin jirgin Sultan Abubakar III.

Kamar yadda labari ya zo mana daga bakin wani Hadimin tsohon gwamna, Attahiru Dalhatu
Bafarawa, Aliyu Magatakarda Wamakko ya rasa ta cewa a lokacin da Mai
gidansa ya rutsa shi. Mai taimakawa tsohon 'dan takarar shugaban
kasar, Nura Aminu Dalhatu, ya bayyana yadda ta wakana tsakanin 'yan
siyasar a filin hjirgin saman Sokoto a Ranar 9 ga Watan Disamban 2019.

Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya yi wa Attahiru Dalhatu Bafarawa
Mataimakin gwamna na kusan tsawon shekaru takwas, amma daga baya ya
sauka saboda tsoron majalisa ta tsige shi. Tsohon gwamna Wammako ya yi
wasu kalamai da su ka batawa Dalhatu Bafarawa rai kwanaki.

Bayan haduwarsu, 'Dan siyasar hamayyar ya maidawa Sanatan na APC martani a
bainar jama'a. "Ka ce ni 'Dan ci-rani ne, meyasa ka ke gaida ni yanzu?
Na san Ubana da Kakana a nan aka haife su, su ka rayu, su ka mutu. Zan
iya kai ka har kabarinsu. Za ka iya kai ni kabarin Kakanka?" Bayan
Bafarawa ya yi wa tsohon Mataimakin na sa wannan tambaya, sai ya yi
gum bai ba ce komai ba.

A wani kaulin an ce Wammako ya sake nanata cewa Bafarawa 'dan cirani ne a Gari. Bayan wannan 'yan takaddama, 'yan siyasar sun hau jirgi guda sun kama hanya zuwa babban birnin tarayya
Abuja. Aliyu Wammako shi ne Sanata mai wakiltar Arewacin Sokoto a
Majalisa.

Aliyu Magatakarda Wamakko ya doke 'Dan takarar da Mai
gidansa ya tsaida a zaben 2007 watau Alhaji Muhammadu Maigari
Dingyadi. Tun daga nan ake ta 'yar tsama har zuwa wannan lokaci.
Previous Post Next Post