Saran Maciji: Abu 3 da ya kamata ka yi idan maciji ya cije ka | ISYAKU.COM

Macizai sun banbanta daga halitta bisa gurbin aji-aji ko rukuni da ke fayyace kalar maciji da tasirin dafi da ke tattare da miyau ko yawunsa. Wasu macizai suna da tsananin dafi kuma cikin minti 15 idan ba a sami dauki ba, bayanai sun ce mutum zai iya rasa ransa.

Mujallar ISYAKU.COM ya samo cewa, wasu macizai suna da saukin dafi ko da sun sari mutum. Amma duk da haka, maciji ba abin da za a yi wasa da cizonsa bane.

Idan aka sami lalurar cizon maciji, abin gaggawa da ya kamata a yi shine:

1- A gaggauta daure sama da kasan wajen da macijin ya sari/ciji mutum, kuma a daure shi sosai domin haka zai hana dafin daga ci gaba da zagayawa cikin jini

2- A tsaga daidai wajen da macijin ya ciza, domin jini tare da dafin ya fita ko ya rage daga ciki.

3- A yanka kosashshen albasa sai a sa barin albasan a daidai wajen da macikin ya ciza.

Yayin da ake gudanar da wannan, a tabbata cewa ana kan hanyar kai wanda macijin ya sara zuwa Asibiti. Wannan kamar taimakon gaggawa ne. Amma a je Asibiti nan take domin ganin Likita.

Masana kan lamarin cizon macizai sun shaida mana cewa, yana da kyau idan da hali a kashe maciji da ya yi cizo, kuma a kai macijin Asibiti tare da wanda macijin ya sara saboda haka zai taimaka wa Likita sanin irin magani ko allura da za a yi nan take daga cikin irin yawan kalolin allurai ko maganin cizon maciji.

Daga Isyaku Garba Zuru,

Aiko Labari, Ra'ayi, ko ka Tuntube mu: Latsa nan >>>

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post