Abin da ya sa ba mu saki El-Zakzaky tare da su Dasuki ba

Sakin Sambo Dasuki da Omowole Sowere ya sa mutane da dama suna tambayar ko yaushe za a saki shugaban mazhabar shi'a ta IMN da gwamnatin Najeriya ta haramta, wato Shaikh Ibrahim El-zakzaky?

To amma Ministan Shari'a na Najeriyar ya ce gwamnatin tarayya ba ta da hurumi na yin katsalandan a wata shari'a da take hannun gwamnatin jiha.

A ranar Talata ne gwamnatin ta bai wa hukumar tsaro ta farin kaya DSS umarnin sakin mutanen biyu, amma ban da El-Zakzaky da shi ma ya dade a hannun hukumomin.

Malami ya kara da cewa: "Saboda haka gwamnatin tarayya ba za ta yi katsalandan a kan shari'a wadda hakkin bibiyarta hakki ne na jiha ba."

Gwamnatin tarayya ta sha bayyana cewa ba ita take rike da El-Zakzaky ba, gwamnatin jihar Kaduna ce take tuhumarsa a gaban kotu.

A baya dai kotu ta bayar da izinin a saki El-Zakzaky da maidakinsa Zinatu, amma hakan ya gagara abinda ya sa ake zargin gwamnatin Najeriya da kin yi wa kotu biyayya.

Ko a ranar 22 ga watan Disamba gwamnatin Amurka ta sanya Najeriya cikin jerin kasashen da za ta sanya wa ido bisa zargin take hakkin kowane mutum na yin addinin da ya ga dama, ba tare da wata tsangwama ba.

Sakataren harakokin wajen Amurka Mike Pompeo ne ya sanar da sanya Najeriya a jerin kasashen.
Rahoton ya ambato rikicin kungiyar mabiya mazahabar Shi'a Sheikh Ibrahim Elzakzaky ke jagoranta, inda Amurka ta ce rundunar sojin Najeriya da hukumomin tsaron kasar na ci gaba da keta hakkinsu na 'yancin gudanar da harkokin su na addini.

A ranar 12 ga watan Disambar shekarar 2015, mabiya mazhabar Shi'a a Najeriya suka hana ayarin da ke tare da Hafsan Sojin kasa Janar Tukur Burutai wucewa Zaria, bidiyon yadda sojojin sukai kokarin sasantawa da 'yan Shi'a don su wuce ya karade kafafen sada zumunta.

An yi arangama tsakanin sojoji da 'yan Shi'a, lamarin da ya janyo asarar rayuka. Tun daga lokacin hukumomi ke tsare da Zazzaky da maidakinsa Zinatu.

Rahotun shafin BBC Hausa

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN