Wani magidanci mai shekara 37 da ya yi ta dukan matarsa har ta mutu ya shiga hannu a jihar Ogun.
A wata sanarwar da mai magana da yawun Rundunar ‘yan sandan jihar DSP
Abimbola Oyeyemi, ya aikewa Aminiya ya shaida cewa jami’an rundunar sun
kame Mutiu Sonola, wanda ake zargi da kashe matarsa Zainab Shotayo a
jiya Laraba bayan da mahaifinta ya kai kararsa ga ‘yan sanda.
Ya ce, Mahaifin marigayiyar ya shaida cewa wanda ake zargin ya dade
yana jibgar matarsa a duk lokacin da dan sabani ya shiga tsakanin su, ya
ce ana ci gaba da bincike akan wanda ake zargin kana za a gabatar da
shi a gaban kotu.
Hakki: Rahotun jaridar Aminiya
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari