Dalilin da yasa har yanzu Buhari bai canja shugabanin tsaro ba - Sanata Ali Ndume

Rahotun shafin Hausa.legit.ng

Dan majalisa mai wakiltar mazabar Borno ta Kudu, Sanata Ali Ndume, ya bada dalilin da suka sa shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai iya sauya shuwagabannin tsaro ba a Najeriya.

Ndume, wanda shi ne shugaban kwamitin majalisar dattijai a kan al’amarin sojin kasar nan, ya sanar da hakan ne a ranar Talata yayin tattaunawa da manema labarai.

An tambayesa dalilin da yasa Shugaba Buhari bai sauya shuwagabannin tsaro ba. Ya bayyana cewa, a halin yanzu Najeriya na zamani ne na yaki. Dan majalisar ya ce, Shugaba Buhari bashi da wani zabin da ya wuce rike shuwagabannin tsaron, ba saboda halin da yankin Arewa maso gabas ke ciki ba kadai, har da dukkan Najeriya.

Ya ce, da sauyin wajen aiki mai karfi, Najeriya zata iya shawo kan matsalar tsaro a jihohi daban-daban na kasar nan kuma zaman lafiya zai tabbata. Ndume y ace: “Muna cikin yaki ne. Yaki babba kuwa.

Muna yakar ta’addanci a Arewa maso gaba da kuwa arewa maso yamma.” Dan majalisar ya ce, Sojin Najeriya sun mayar da hankali ba kadan ba wajen shawo kan matsalar rashin tsaro na kasar nan. Ndume ya kara da bayyana cewa, zai yi aiki da mataimakin shugaban majalisar dattijai Omo Ovie-Agege don tabbatar da ‘yan Najeriya sun samu irin aiyukan da suka kamata.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN