Duba ababen alhairi 34 da wani dan majalisan tarayya ya yi wa jama'arsa a kudancin jihar Kebbi

Daga Jadawalin Nasarorin da Dan Majalisar Wakilai Mai Wakiltar Yawuri, Shanga da Ngaski Alhaji Dakta Yusuf Tanko Sununu ya samu zuwa karshen wannan Shekarar 2019 mai karewa:

Daga Real Sani Twoeffect Yawuri.

Daga Cikin jadawalin kokarin da dakta Sununu yayi wajen ciyar da al'ummar mazabunsa gaba kamar haka:

1. Yayi nasarar tsamo wasu matasa akalla goma sha biyar (15) masu zaman kashe Wando a karamar hukumar Ngaski daga zaman banza zuwa makaranta da kuma koyawa wasu daga cikinsu sana'ar hannu

2. Ya kaddamar wani gangami na ceto akalla mutum Dari biyar (500) daga matsalar idanu inda akalla ansamu nasarar yiwa mutum Dari daya (100) tiyatar idanun daga cikin kaso biyu na gangamin da ya gudana a kananan hukumomin Yawuri, Shanga da ingaski

3. Yayi nasarar samarwa wasu yan asalin mazabunsa mutum biyu aikin gwamnati wato Jamilu Sani da kuma Abdullahi Haruna

4. Ya samar da Injimin Markade/nikan gari ga al'ummar garin Runtuwa

5. Ya samar da hanyoyin da akabi wajen samar da taransifomar wutar lantarki domin gyara wutar lantarki a garin Ngaski

6. Ya gina wasu rijiyoyi tareda jan layin kan famfo da zai samar da a unguwanni ko wurare daban-daban na dibar ruwa cikin sauki ga al'ummar garin Mararrabar Yauri,  dake karamar hukumar Ngaski

7. Ya kafa kwamitoti da zasu binciko matsalolin dake addabar yankin masarautar Yawuri da yake wakilta domin samar da hanyoyin da za'a magance su

8.ya biyama daliba Habiba ingaski kudin rajistareshin na kudi naira dubun hamsin #50,000  dake ajin karshe a makarantar koyon Aikin jinya dake jega ( college of health technology jega) domin kammala karatunta.

9.Yayi nasarar dakatar yajin aiki malaman Asibiti har sau uku tare da kakakin majalisa Femi Abdulhakeem bjabiamila na share awa biyu ana tattaunawa

10.Ya jagoranci kawo karshen badakalar likitoci akan yajin aiki su da bashin kudi 26.5 billiyan da suke bi na arriyas

11.sannan ya raba raguna ga mazabunsa guda talatin (30) domin hidimar sallah

12.ya gina kwalbati a yelwa ta tsakiya wato (Yelwa Central)

13.Ya rubuta takarda Zuwa ga kamfanin MTN domin Samar da sabis a garuruwan birnin Yawuri, Utono dake karamar hukumar mulki ta ingaski,da kuma Dugu dake karamar hukumar mulki ta Shanga

14. Ya ziyarci Al'ummar Garin Hundeji dake karamar hukumar mulki ta Shanga da yake Wakilta domin jajanta musu akan iftila'in  Ambaliyar ruwan sama da ya fada musu,wanda yayi sanadiyar hasarar gidaje da gonaki,inda ya basu tashi gudunmuwa.

15.A matsayinsa na shugaban kwamitin lafiya na majalisar wakilai ya jagoranci kawo karshen badakalar Amshe lasisin tsangayar karatu na jami'ar  Ahmad bello dake zariya,a cikin awanni arba'in da takwas a kasa da awa shida da sheda masa

16.kakakin majalisar wakilai Femi Abdulhakeem bjabiamila ya karramashi a zauren majalisa bisa kokarin sa na kawo karshen rikice rikice na malaman Asibiti.

17.Daliban masu koyon Aikin jinya da Ungozoma sun karrama dakta sununu bisa kokarin sa na kawo karshen badakalar su.

18.Dakta sununu yakai kudiri a zauren majalisa akan yadda za'a samar da sauye sauye da kuma kira ga gwamnatin Tarayya domin Samar da cibiyoyi na masu kula cutar daji  wato (Cancer) Kansas a fadin dukkan kananan hukumomin najeriya.

19.Dakta sununu yakai kudiri a zauren majalisa akan yadda za'a samar abinci wadatacce a Najeriya Kamar Haka:-
1.samuwar abincin Kansa

2. Yanayin da za'a iya samun abincin
 da kuma iya sayensa ga kowa
3.kasuwa da yanayi mai kyau da za'a iya sayar dashi.

20.Dakta sununu ya kai kudiri a zauren majalisa akan yadda za'a shawo matsalar barayin shanu da masu satar mutane da garkuwa dasu domin neman kudin fansa a jihohin  arewa maso yamma musamman katsina, Zamfara,da sokoto.

21. Dakta sununu ya kai kudiri a zauren majalisa Wanda yayi Kira da'a cire takunkumi akan daukar likitoci aiki a gida Najeriya ganin yadda likita guda zai kula da mutum talatin ko fiye da Haka.

22. Dakta sununu ya bada Tallafin Naira dubu Dari hudu domin samawa dalibai yan asalin masarautar Yawuri wurin Zama a yayin karatun su a jami'ar kimiya da fasaha dake Alairu (Ksusta)

23.Dakta sununu ya Samar da wurin Zama na akalla mutum arba'in domin samun sauki a karatun su a jami'ar gwamnatin Tarayya dake birnin kebbi wato(FUK)

24.Hakama dakta sununu ya bada Tallafin Naira dubu Hamsin hamsin ga dalibai masu karatun digiri na biyu dana uku yan asalin masarautar Yawuri dake jami'oi daba-daban a fadin Najeriya.

25. Dakta sununu yayi kokari wurin samama dakta habibullah Adamu aiki a ma'aikatar lafiya mataki na farko wato(National Primary health Care development agency)

26. Dakta sununu a karon farko ya samoma mutanen kananan hukumomin Yawuri Shanga ingaski Tallafi daga kungiyar bada Tallafin agajin gaggawa ta kasa tare data jiha wato sema,wadanda iftila'in Ambaliyar ruwan sama ya fadama daminar data gabata.

27.Dakta sununu ya iya bakin kokarin sa a matsayinsa na wakili mai wakiltar kananan hukumomin Yawuri Shanga ingaski akan matsalar gyaran Hanya na gwamnatin Tarayya daga Yawuri Zuwa koko,na fadi tashin ganin an kammala wannan Aiki.

28.Dakta sununu ya gyara fomfon Unguwar akwanga dake karamar hukumar mulki ta ingaski,wanda suka share watannin suna fama da matsalar ruwan Sha.

29.Hakama dakta sununu ya tallafawa marassa lafiya da kudin magani wanda bazan iya kawo adadin su ba,hakama ya tallafawa marassa lafiya a matsayinsa na tsohon likita domin basu kulawar gaggawa.

30. Hakama muma Yan (social media) wato kafar sadarwa ta zamani yana fadi tashin ganin ya samama wasun mu ayukkan yi da kuma Samu musu hanyar  sana'oin dogaro dakai.

31. Hakama Dakta na cigaba gyaran Asibitin Garin gebe da fadada shi dake karamar hukumar mulki ta Shanga.

32. Hakama Dakta ya Samar kujerun APC party office na garin Yawuri.

33.Dakta sununu Yanzu haka yana gab da sanya fitilun Sola a garin Shanga.

34. Dakta Yusuf Sununu ya dauki nauyin yara guda goma Sha biyu, Kuma ya biya kudin karatun su s makarantar Abdullahi Yaba.

Wadannan ababe ne da suke nunawa karara yadda wannan bawan Allah yake tsaye kyam wajen ganin ya samar da cigaba a yankinsa wanda cikin Dan kankanin lokaci da hawansa kujerar har yayi wannan nasarar dana tsakuro muku.

Kuma babu aiki ko daya daga Gwamnatin Tarayya data ke bayawar wanda 'yan majalisa keyiwa mazabunsa wato (project continuecy)

Muna masa addu'ar Allah ya dafa masa ya cigaba da samar da ayyukan alheri ga Jama'arsa,  Amin


DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN