Hakimin Birnin Gwari ya kubuta daga hannun wadanda suka yi garkuwa da shi

Rahotun Jaridar Aminiya

Hakimin Birnin Gwari kuma Sarkin Kudun Birnin Gwari Alhaji Yusuf Yahaya Abubakar, wanda aka yi garkuwa da shi kwanaki takwas da suka gabata ya kubuta daga hannun masu garkuwan.

Ya kubuta ne a daren ranar Alhamis din nan zuwa wayewar garin yau Juma’a a wani kauye Sabon Birni inda ake rike da shi.

Aminiya, ta samu bayanin cewa duk da ‘yan uwansa sun biya kudin fansa na Naira miliyan 3.5, amma sun ki sakinsa har sai da Allah ya kubutar da shi ta hanyar guduwa.

Wakilinmu ya ziyarci gidansa da ke a Kaduna inda ya tarar da ‘yan uwa da abokanen arziki cike da suka je  taya shi murna.

“Allah ne kurum ya kubutar da mu dan haka ina wa Allah  Godiya matuka da Ya sa har na dawo gida lafiya,” in ji shi.

Sarkin Kudun ya kuma ce shi ba zai ce komai ba dangane da halin da ya shiga illa kurum ya mika godiyarsa ga Allah.

Shima wanda aka sace su tare a makon jiya watau tsohon sakataren ilmi a Birnin Gwari watau Ibrahim Musa, shima an ce an sako shi kwana biyu da suka wuce.

Sai dai babu bayanin ko am biya kudin fansa kafin a sake shi.

Mukaddashin Gwamnar jihar Kaduna Aminu Shagali, ya ziyarci gidan Sarkin Kudun, inda ya jajanta masa.

Credit: Rahotu da hoto daga Jaridar Aminiya
 
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN