Jarumin finafinan Bollywood Kushal Punjabi ya kashe kanshi, karanta dalili

Fitaccen Jarumin masana'antar finafinai na kasar India Bollywood, Kushal Punjabi mai shekara 37 ya kashe kanshi ranar 26 ga watan Disamba 2019 a gidanshi da ke Mumbai ranar Alhamis.

Wata kafar labarai a Mumbai ta ruwaito cewa an ga gawar Kushal tana lilo a cikin gidansa, a yanayi da ake kyautata zaton cewa Jarumin ya rataye kanshi ne.

Wani abokin Kushal mai suna Karanyuir Bohra ya ruwaito mutuwar Jarumin a shafinsa na sada zumunta, inda ya kara da cewa za a gudanar da jana'izar Jarumin ranar Juma'a da karfe 4 na yamma a Mumbai.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN