Yansandan jihar Katsina sun yi ram da kungun wasu barayi

Rundunar yansandan jihar Katsina ta cafke yan gungun wasu barayi da suka kware wajen satar kudi da wayoyin salula da sauran ababen amfani daga bayin Allah.

Sanarwar haka ta fito ne a wata sanarwa daga Kakakin hukumar yansanda na jihar Katsina SP Isah Gambo ranar Lahadi 10 ga watan Nuwamba, ya kara da cewa rundunar tana ci gaba da gudanar da bincike akan zargin kisan kai da ake zargin yan gungun da aikatawa.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post