Duniya kenan: An raba gadon dukiyar marigayi Rabilu Musa Ibro

Legit Hausa
Kamar yadda tashar tsakar gida ta samo daga jaridar yanar gizo ta Najeriya arewa a ranar Alhamis 1 ga watan Agustan da ya gabata na wannan shekarar, anyi rabon gadon jarumi Rabilu Musa dan Ibro da ya kwanta dama shekaru biyar da suka gabata.
Marigayin dan wasan barkwancin ya bar tsabar kudi a asusun ajiyarsa na bankin Union har naira miliyan 30. Marigayin ya bar motocin tirela biyu da bus guda biyu. Ya mallaki gida daya a Gwarinpa Abuja. Ya mallaki gidajen siyar da man fetur 2, daya a Wudil, dayan kuma a titin Yola a Kaduna. Akwai kuma gidan da yake aikin gininsa ba a kammala ba.
Marigayin ya rasu ne a ranar 9 ga Disambar 2014. Mutuwarsa na daya daga cikin manyan rashi da aka yi wanda ta girgiza masana'antar Kannywoodbayan rasuwar marigayi Ahmad S. Nuhu wanda ya rasu yana tsaka da tashensa a masana'antar. Rasuwar kuwa ta jefa mutane da dama cikin alhini da jimami.
Kafin marigayin ya kwanta dama, shine shugaban 'yan fim din arewa da harkar camama.
An haifi marigayi dan Ibro ne a garin Dan Lasan dake karamar hukumar Warawa dake Kano. Ya rasa rasu ne sakamakon fama da ciwon hanta da yayi. Ya rasu yana da shekaru 47 a duniya inda ya bar mata 3 da 'ya'ya ashirin.
Allah ya jikan marigayin jarumin barkwancin ya kuma sa aljanna makomarsa.
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN