Miye dalili: Wata budurwa ta sha dan karen duka a wajen saurayinta

Wata mace mai suna  Odirile Didi Moeletsi ta ce ta sha dan karen duka daga wajen saurayinta, lamari da ya sa fuskarta ya kumbura kuma jini ya kwanta a kumatunta.

Ta ce lamarin ya faru ne ranar Asabar da dare.

" Na sha dan karen duka daga wajen saurayi na, ya ce yana kaunata da gaske kowane rana, amma a jiya da dare kam, wannan soyayyan ya bayyana a zahiri , Katlego Mashifane, wadanda basu san shi ba, lallai mutumin banza ne, mai yawan cin zarafi da zagi, mara mutunci ne".DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post