Samun maziyarta fiye da 3.7m isyaku.com ya tsara gabatar da tallace tallacenku

Mujallar ISYAKU.COM ta sami maziyarta shafinta har fiye da mutum Miliyan uku da dubu dari bakwai, adadi da ke karuwa a kullum. Sakamakon haka ISYAKU.COM ya zama wuri da za ka fadi ra'yinka, ko isar da sako cikin tsari da ladabi ga yan siyasa ko mahukunta dangane da lamari da ya shafi al'umma.

Hakazalika, Mujallar ISYAKU.COM ya inganta sashensa na Tallace tallace da sanarwa a shafinsa na yanar gizo, domin mai karamin karfi ya amfana da tsarin sadarwar zamani na intanet.

Daga yanzu, ISYAKU.COM zai dinga zagayawa ciki da wajen garin Birnin kebbi da kewaye, kananan hukumomi, har da makwabtan jihohi domin samun ra'ayin jama'a zahiri daga inda suke domin sanar da mahukunta halin da talakawanta suke ciki daga bakin su talakawan kai tsaye domin haka zai taimaka wa mahukunta wajen tsare-tsare na abbaben da ke da muhimmanci ga rayuwa da ma'amala da zamantakewan  talakawa.

Muna kuma maraba da shawarwarinku kamar yadda aka saba, kuma mun shirya tsaf domin fara wallafa shawarwari, ko ra'ayoyinku ta hanyar samar da gurbin ingizon haka a shafinmu.

Mun gode.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post