Yadda yan Tauri suka burge jama'a wajen wani wasa a Masarautar Argungu

Wasu masu wasan Tauri sun yi ta kokarin caka wa cikinsu karafa masu tsini a wajen wasan Tauri lokacin wani bikin nadenaden Sarautar gargajiya, amma karfen ya kasa hudasu a garin Bachaka da ke karkashin Masarautar Argungu a Arewacin jihar Kebbi ranar 10/12/2017.Masarautar Argungu a jihar Kebbi, tana da kayakin tarihi tun zamanin Sarki Kanta, hakazalika har yanzu wasu al'adun gargajiya kan wanzu daga lokaci zuwa lokaci a wajen tafiyar da wasu bukatu na rayuwa tsakanin al'umman wannan Masarauta da kewaye, kamar yadda yake a kasar Hausa.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post