Labari cikin hotuna: Duba abin da mabiya Shi'a suka yi a jihar Kebbi

Mabiya akidar Shi'a a jihar Kebbi, sun gudanar da Muzaharar Maulidi da sanyin safiyar Juma'a 22 ga watan Nuwamba a garin Birnin kebbi.

Muzaharar  wanda har da mata da kananan yara, sun zagaya daga Titin Makerar Gandu suka biyo ta tagwayen Titin Majalisa, daga bisani suka ketara ta Titin Ahmadu Bello zuwa Shataletalen Sir Yahaya a garin Birnin kebbi.

Tuni dai gwamnatin tarayya ta haramta kungiyar IMN, amma Lauyoyin kungiyan sun garzaya Kotu domin kalubalantar mataki da gwamnatin tarayya ta dauka na haramta kungiyan.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post