Makauniya ta rubuta Qur'ani daga Bakara har Nasi

Legit Hausa
Wata mata 'yar asalin kasar India mai fama da cutar makanta ta rubuta Al-Qur'ani mai girma daga Bakara har Nasi da rubutun Braille.
Nafees Tasreen, malama ce a wata makarantar gwamnatin a India, ta kasance mai kwazo da sadaukarwa a harkokinta.
Kamar yadda Nafees Tasreen ta ce, a lokacin tana kwaleji, tana da son karanta Qur'ani amma bata samu malamin da ke son koyawa makauniya karatu ba.
Amma daga baya ta samu Hafiz Mohammed Tasleem kuma ya amince da zai dinga koya mata. A lokacin da take koyon karatun Qur'anin, ta nuna bukatar koyon rubuta Qur'ani da yaren Braille don taimakawa makafi irinta. Ta maida hankali wajen kokarin taimakon makafi irinta wajen karatu da fahimtar Qur'ani.
Nafees Tasreen ta dau shekaru uku ne wajen rubuta Qur'ani tare da fassarar sa a yaren Hindi. Bayan kammala rubuta Qur'ani, ta dau lokaci ana duba mata kura-kurenta.
Babban malamin kasar India ya jinjinawa aikinta kuma ya tabbatar da babu kura-kurai a duk surorin da ta rubuta.
Braille dai yanayin rubutu ne da Louis Braille ya kirkiro dashi wanda ke ba makafi damar rubutu da karatu.
Hakazalika, musulmai da yawa sun yarda cewa nakasa jarabawa ce daga Allah a rayuwa kuma zata iya zama baiwa a wani bangaren. Akwai bukatar duk mai nakasa ya kasance mai hakuri kuma a daina waresu don duba daga cikin wani bangare na al'umma.
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post