Yansanda sun dakile yunkurin fashin motar daukan kudi daga bankin CBN a Benin

Yansanda a birnin Benin, sun yi nassarar dakile wani yunkurin fashi da makami a babban Bankin Najeriya bayan wasu yan fashi sun far ma Bankin ranar Talata.

Wannan mumunar lamari ya faru ne a tsakiyar birnin, watau King Square. Rahotanni sun ce yan fashin wadanda a shirye suke, sun yi kokarin kwace wata motar daukan kudi ne da ke daf da fitowa daga Bankin CBN dauke da kudi zuwa wani Banki .

Sai dai jami'an tsaro da ke bankin su nuna wa yan fashin kwarewarsu, bayan barin wuta da bindigogi tsakanin jami'an tsaro da yan fashin na tsawon wasu mintoci, daga bisani yan fashin sun gudu.
 
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post