An ceto wata mace da dan uwanta ya kulleta a wani daki har shekara 2

Yansanda a jihar Kaduna sun ceto wata mata wacce dan uwanta na jini ya rufe ta a cikin wani daki mai duhu har tsawon shekara biyu.
Yansanda tare da wata kungiya mai zaman kanta, Arida Relief Foundation ne suka gano matar mai suna Hassana Sale a cikin wani mawuyacin yanayi mai ban tausayi a unguwar Rigasa da ke jihar Kaduna.
Dan uwan Hassana mai suna Lawal ne ya rufeta a dakin, domin yan uwanta basa son yadda take zuwa gidan tsohon mijinta domin duba yaranta guda hudu bayan ya sske ta.Tuni dai yansanda suka kama Lawal. 
Shugaban kungiyar da ke bin diddigin lamarin Hajiya Rabi Salisu, ta ce Hassana na cikin matsanancin damuwa bayan mijinta ya sake ta, sakamakon haka take zuwa gidansa dimin ta gan yaranta kafin dan uwanta ya kulleta a cikin daki mai duhu.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post