Labari cikin hutuna: Wata mata ta rasu da kalmar shahada a bakin Masallacin Juma'a

Gawar Aisha (Cididu)
Wata tsohuwa baiwar Allah mai suna Aisha wadda aka fi sani da suna Cididu wacce ke unguwar Illela Yari a garin Birnin kebbi, ta sami cikawa da kalmar shahada a bakin babban Masallacin Juma'a na jihar Kebbi kafin Sallar Juma'a ranar 1 ga watan Nuwamba 2019 da misalin karfe 1:15 na rana.
Yan agaji na rufe kofar inda Aisha ta rasu kafin a dauki gawarta

Mujallar ISYAKU.COM ya tabbatar da haka bayan wata gajeruwaar ganawa da wata tsohuwa mai suna Igen Na'uwa da ke unguwar Tudun wada a garin Birnin kebbi wacce ganau ce ba jiyau ba da lamarin ya faru a gabanta, ta shaidaa mana cewa;
Wasu mata da Aisha ke tar da su a bakin kofar shiga Masallaci kafin rasuwarta


"Abin da na gani shine muna zaune sai ta fara tari, sai ta rike ni kwarai ta ce mani ina jin bana da lafiya, nima na rike ta sosai, sai ta ce waiyo! waiyo!! har sau biyu, sai na ce Inna lillahi wa'inna ilehi raji'un na sake maimaitawa, sai ta karba ta ce Inna lillahi wa'inna ilehi raji'un , Allah ya bata ikon fadin haka, sai na ce La ila ha illallah Muhammadu rasurullahi  sallallahu alaihi wasallam, ita ma Allah ya bata ikon fadin haka, duk abin da na fada shi ne ta maimaita.

"Daga nan sai sarin jini da gudajensa ya dinga fitowa daga bakinta, sai wani bawan Allah ya zo ya taimaka mana aka kaita gefe aka kwantar da ita, daga nan Allah ya yi mata cikawa, bakin abin da na sani kenan"
Wata tsohuwa cikin alhini bayan rasuwar Aisha

Mujallar ISYAKU.COM da duk ma'aikatanta, muna yi wa Mama Aisha addu'ar Allah ya karbi bakoncin ta ya sa ta cikin rahamarsa, ya sanyaya mata, ya yafe mata kura-kurenta, ya saka ta a Aljannah Firdaus. Mama Aisha ta sami kyakkyawan karshe, Allah ya  sa mu cika da imani idan tamu ta zo. Amin.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
 • Previous Post Next Post

  Reported by ISYAKU.COM

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
  https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
  LATSA NAN 

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

  Facebook.com/isyakulabari