Bidiyo: Dan sanda ya turo budurwa daga saman bene saboda ya ce ta sanya Hijabi a jikinta taki sakawa

Legit Hausa

Wani bidiyo da ya fara yawo a shafukan sadarwa ya nuna yadda wani dan sanda na kasar Iran ya turo wata matashiyar budurwa daga saman bene saboda taki amincewa ta sanya Hijabi.
A bidiyon wanda wani dan jarida mai suna Masih Alinejad ya wallafa, ya bayyana yadda budurwar ta shiga wani waje mai suna Shahr-e-Rey, inda wani dan sanda ya nemi ta tsaya taki tsaya ta cigaba da tafiyar ta.
Wannan abu da tayi ya harzuka dan sandan inda ya ture ta kasa sannan ya naushi wani mutumi a haba a lokacin da ya zo ya kawo mata dauki.
A ka'idat dokar shari'ar musulunci ta kasar Iran, dole ne mace ta rufe gashin kanta kada maza su gani, sai dai kuma matan sun fara fito suna nuna rashin goyon bayansu akan wannan doka da aka sanya.
Ga dai bidiyon yadda lamarin ya kasance a kasa:
/div> DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post