Bidiyo: An kama almajirai da suke yaudarar mutane ta hanyar sanya ciwon karya a jikinsu don a basu sadaka


Legit Hausa

An kama wasu mabarata a jihar Legas da suke hada ciwon karya suna yaudarar mutane da shi ana ba su sadaka. A wani bidiyo da @gidifeedtv ta wallafa a shafin Twitter yau Alhamis dinnan, namijin da aka kama an tilasta shi ya cire duka kayan da yake amfani da su wajen hada wannan ciwo na shi.

Har ya zuwa yanzu dai ba a san ainahin inda wannan lamarin ya faru ba a jihar ta Legas, kuma ba a san kowanene mabaracin ba. Tsananin talauci da yunwa ta sanya mutane na kara fita yawon bara da almajiranci, inda a yanzu haka ake hasashen cewa almajiran da suke bara a yanzu sun linka wadanda suke a baya.

Ga dai bidiyon yadda lamarin ya kasance a kasa:DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
 • Previous Post Next Post

  Reported by ISYAKU.COM

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
  https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
  LATSA NAN 

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

  Facebook.com/isyakulabari