Kwanan nan shinkafa za ta yi arha ta yadda ba za ta fi karfin talaka ba – Gwamna Bagudu

Legit Hausa
Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi ya ce albarkar da aka samu a fannin noma shinkafa a wannan daminar zai taimaka wajen daidaita farashin shinkafa a kasuwannin Najeriya.
Bagudu, wanda ya kasance Shugaban kungiyar haraji na Shugaban kasa kan shinkafa da alkama a kasar, ya bayyana hakan a wani jawabi da ya yi a ranar Litinin, 4 ga watan Nuwamba a karamar hukumar Argungu da ke jihar a yayinda yake zantawa da manoman shikafa a yankin.
“Albarkar da manoman shinkafa suka samu a wannan daminar zai karya farashin shinkafa yar gida domin hana fasa kaurin shinkafa yar waje cikin kasar da kuma samar da farashi mai rahusa ta yadda talaka zai iya siya,” inji shi.
Bagudu ya fada ma manoman shinkafa cewa kwanan nan gwamnatin jihar za ta fara samarwa tare da raba masu kananan injinan casar shinkafa, domin bunkasa ingancin shinkafar da suke kaiwa kasuwa.
“Tuni aka horar da matasa akan aiki da injinan wanda za su isar da wannan ilimi ga manoman shinkafa a kananan hukumomi 21 da ke jihar,” inji Bagudu.
Daya daga cikin manoman, Alhaji Abubakar Usman, ya fada ma gwamnan cewa sun samu girbi mai tarin yawa a wannan shekarar sannan cewa zai isa har zuwa badi.

Usman ya kuma roki gwamnatin jihar da ta taimaka masu da taki, maganin kashe kwari da kuma injinan casar shinkafa.
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN