Kotu ta tabbatar wa matawalle kujerarsa, ta ci tarar masu kara

Legit Hausa
Kotun sauraron kararrakin zaben kujerar gwamnan jihar Zamfaradake zama a Abuja, tayi watsi da karar da ke bukatar sauke Gwamna Bello Matawalle daga kujerarsa a ranar Litinin.
Karar da Muhammed Takori na jam'iyyar APDA ya shigar akan Matwalle da hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC an yi watsi da ita ne a yau.
Takori da jam'iyyar APDA sun shigar da karar ne da bukatar a sauke Matwalle daga kujerar gwamnan jihar saboda bai ci kuri'u biyu bisa uku na jimillar kuri'un jihar kamar yadda doka ta tanadar.
Amma yayin yanke hukunci, kotun sauraron kararrakin zaben da ta samu jagorancin Jastis Binta Zubair, ta yanke hukuncin cewa karar bata da makama kamar yadda kotun koli ta bayyana tun a ranar 24 ga watan Mayu, 2019..
Zubair ta kara da cewa, kuri'un da PDP ta samu a zaben 9 ga watan Maris a jihar Zamfara sune halatattun kuri'u a zaben gwamnan.
Kotun bata aminta da ikirarin masu kara da suka ce Matawalle bai lashe kashi biyu cikin uku na kuri'un duk kananan hukumomin jihar ba
Tun farko kotun sauraron kararrakin zaben ta yi watsi da ikirarin Takori da yace PDP bata yi zaben fidda gwani ba kuma jam'iyyar bata dau nauyin Matawalle ba a don haka bai dace da takarar gwamnan jihar ba tun da farko.
A don haka ne mai shari'ar ta yankewa masu karar tarar naira dubu dari biyar da zasu biya Matawalle.
Idan zamu tuna, hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC ta bayyana Mukhtar Idris na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Zamfara a zaben 9 ga watan Maris da aka yi.
A sakamakon rashin yin zabe fidda gwani kamar yadda shari'a ta tanadar, kotun koli ta kwace kujerar ta mikawa Bello Matawalle na jma'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben. Ta bayyana kuri'un da jam'iyyar APc ta samu a matsayin asarar kuri'u
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post