El-Rufai ya bayar da umarnin biyan ma'aikata bashin sabon karin albashi

Legit Hausa
Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufai, ya bada umarnin biyan kusan malaman firamare 8,500 cikin 39,000 da gwamnatin jihar ta dauka aiki, basussukansu cikin satin nan.
A takardar da mai ba gwamnan shawara na musamman akan yada labarai, Muyiwa Adekeye, ya bada a ranar Asabar, gwamnan ya nuna rashin jin dadinsa ta yadda kananan hukumomin suka rikewa malaman makarantar.
Hakan kuwa ya faru ne da malaman makarantar firamarin da aka dauka kashi na biyu a jihar.
"Bayan bayani daga ma'aikatar kanananan hukumomi da SUBEB, gwamnatin jihar ta gano cewa kananan hukumomi suna rike da kusan naira miliyan 1.8 na albashin malaman makarantar da aka dauka a karo na biyu. Albashin ya hada daga na watan Janairu zuwa Mayu 2019," in ji takardar.
Gwamnan El-Rufa'i ne gwamna na farko da ya fara biyan ma'aikatan jiharsa sabon karin albashin da shugaba Buhari ya saka wa hannu bayan samun sahalewar majalisun kasa.
Sai dai, sauran gwamnoni sun bayyana cewa zasu biya sabon karin albashin ne daidai da karfinsu, watau ba lallai ya kasance N30,000 zasu biya ma'aikatan jihohinsu ba a matsayin mafi karancin albashi.
Tuni kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta bayyana rashin amincewarta da wannan mataki da gwamnonin suka dauka, inda suka bayyana cewa duk gwamnan da ya gaza biyan mafi karancin albashin kamar yadda doka ta amince, zai fuskanci yajin aiki a jiharsa.
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
 • Previous Post Next Post

  Reported by ISYAKU.COM

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
  https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
  LATSA NAN 

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

  Facebook.com/isyakulabari