Jami'an tsaron Osinbajo sun yi wa dan Jarida dan banzan duka, karanta dalili

Legit Hausa

A yau ne wasu jami'an tsaro dake gadin mataimakin shugaban kasa
Farfesa Yemi Osinbajo suka sauke fushinsu a kan wani dan jarida mai
daukan hoto dake aiki da gidan jaridar Vanguard, inda suka lakada masa
dan banzan duka.aridar

The Cable ta ruwaito lamarin ya faru ne a cikin
fadar gwamnatin Najeriya, Aso Rock Villa, yayin da Osinbajo ya halarci
taron hukumar kula da yan Najeriya mazauna kasashen waje daya gudana a
babban dakin taro na Villa.

A wannan lokaci ne dan jaridar mai suna
Adeshida Abayomi ya tsaya yana daukan mataimakin shugaban hotuna,
kwatsam sai ya ga jami'an hukumar tsaro na DSS sun far masa, suka
shiga dukansa, suna jan shi a kasa, tare da farfasa masa na'urar
daukan hotonsa.

Duk wannan lamari ya faru ne a gaban mataimakin
shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, amma ko uffan bai ce ba, babu
abin da ya yi domin ya hanasu, sai dai babban dogarinsa ne ya sa baki
suka kyale ni. "Na yi mamaki a lokacin da jami'an DSS suka diran min
da duka babu gaira babu dalili. Suka kekketa shaidar izinin shigata
Villa, suka dinga ja na a kasa yayin da suka jibgata, suna harbi na da
kafafuwansu.

A yanzu haka duk jikina ciwo yake, musamman kafata ta
dama. "Basu daina dukana ba har sai da babban dogarin mataimakin
shugaban kasa yasa baki, wanda na yana nuna musu da hannu a kan su
kyale ni." Inji shi. Duk kokarin da majiyarmu ta yi na jin ta bakin
kaakakin Osinbajo, Laolu Akande, amma hakan ya ci tura.

A wani labari kuma, an samo cikakken jerin sunayen hadiman mataimakin shugaban kasa
Farfesa Yemi Osinbajo da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sallama
daga aiki, tare da mukamansu Daga cikin su akwai Ajibola Ajayi, diyar
tsohon gwamnan jahar Oyo, Isiaka Abiola Ajimobi wanda it ace hadimar
Osinbajo ta musamman a kan harkar shari'a, Lanre Osinbona, babban
mataimaki na musamman a kan sadarwar zamani, Imeh Okon babban
mataimaki na musamman a kan manyan ayyuka.
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN