Da duminsa: Kotu ta tabbatar wa Okorocha da kujerarsa

 Legit Hausa

Kotun daukaka kara da ke Owerri a ranar Alhamis ta jaddada nasarar
Sanata Rochas Okorocha, a zaben sanata mai wakiltar mazabar Imo ta
yamma da ta gabata. Shugaban kungiyar alkalan, R. A Ada, wanda ya
karanto hukuncin, yace daukaka karar da Osita Izunaso na jam'iyyar
APGA da Jones Onyereri na jam'iyyar PDP suka yi ta kalubalantar
nasarar Sanata Okorocha bata da makama.

Alkalin ya tabbatar da hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben akan shari'ar Okorocha din.
Yace shari'ar bata da matsala kuma kotun daukaka kara ta yarda da ita.
Kungiyar alkalan tace, karar ta kasa bayyana gamsassun shaidu akan
zargin magudi, cika kuri'u, canza sakamakon zabe da kuma kwace
sakamakon daga hannun ma'aikatan zaben.

Mai shari'ar yace, karar ta kasa bada shaidu akan barazanar da aka yiwa jami'in INEC mai bayyana
sakamakon zaben har ya sanar cewa Okorocha ne ya lashe zaben. A ranar
23 ga watan Fabrairu ne Okorocha ya kada Onyereri da Izunaso amma sai
jami'in da ya sanar da sakamakon zaben yace anyi mishi barazana ne
sannan ya sanar da sakamakon zaben.
Previous Post Next Post