Duba hoto da sunayen dalibai 8 da jami'ar Taraba ta kora bisa dalilin kungiyar asiri

Mahukunta a Jami'ar jihar Taraba, sun kori wasu dalibai wanda hukumar Jami'an ta same su da laifin kasancewa cikin kungiyar asiri (Cultism).

Mujallar isyaku.com ya samo cewa rahotun wani fada tsakanin yan kungiyar asiri ya isa wajen mahukuntan Jami'ar ranar Litinin 18 ga watan Nuwamba.

Jami'ar ta sami daliban da laifuka da suka hada da kawo tashin hankalai acikin Jami'ar, fitina, da sauran dabi'u da Jami'ar ta haramta.

Hakazalika an dakatar da daliban daga shiga cikin Jami'ar nan take.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post