• Labaran yau

  DSS da FRSC sun damke wanda ya kera lambar motar "Chip Whip"

  Legit Hausa

  Hukumar kiyaye hadurra da hukumar jami'an tsaron farin kaya sun cafko
  wadanda suke hada lambobin mota na bogi a jihohin Kano da Kebbi. Daga
  cikin wadanda aka cafken akwai wadanda suka hada lambar motar 'Chip
  Whip'. Lambar motar da aka danganta da bulaliyar majalisar jihar Kano
  ta jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta na zamani. Babban jami'in
  hukumar kiyaye hadurra,

  FRSC, Boboye Oyeyemin, ya umarci Zubairu Mato,
  shuagaban hukumar a jihar Kano, su hada kai da jami'an tsaro don gano
  wadanda ke hada lambobin motar na bogi a jihar.

  Ya ce, jami'an tsaron farin kaya a jihar Kano, tuni suka bazama don binciko masu wannan
  aiki. "A ranar 12 ga watan Nuwamba ne, jami'an tsaro na fararen kaya
  suka kai samame Sabon Gari, Kofar Ruwa, Gidan Boss wato Kofar Mazugal,
  Kofar Wambai ('Yan Robobi) da Naibawa titin Zaria," in ji shi. "A
  Sabon Gari, an cafko wanda ake zargin ne inda daga baya aka mikasa
  gaban kotu. Lokacin da aka kama wanda ake zargin, yana kokarin haka
  rami ya boye haramtattun lambobin motar da yake hadawa don ya gujewa
  kamen." a cewarsa.

  "An gurfanar da wadanda ake zargin gaban kotun
  majistare a ranar Juma'a a Birnin Kebbi. Duk da sun musanta aikata
  laifin da ake zarginsu, alkalin ya bukaci da a cigaba da tsaresu har
  zuwa ranar 28 Nuwamba 2019 inda za a cigaba da sauraron karar," in ji
  shi.
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: DSS da FRSC sun damke wanda ya kera lambar motar "Chip Whip" Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama