Allah mai iko: Wata mata ta haifi jariri a cikin keken Napep - Hotuna

Wata mata ta haihu a cikin adaidaita sahu watau Vespa a birnin Lagos bayan Asibiti mai zaman kansa da ta je sun ki karbarta saboda sarkakiya da halin da take ciki lokacin nakuda, sakamakon haka suka turata zuwa Asibitin Gwamnati.

Amma kafin ta isa ne, sai kan jariri ya fito kuma mahaifa ya laulaye wuyan jaririn, ganin haka ke da wuya sai mai adaidaita sahu ya tsayar da adaidaita sahu ya sauka ya tsere ya bar matar a hannun Allah, ita kuma ta dinga ihu.

Daga bisani wani Unguwarzoma ko Nurse, na miji, mai suna Edeaghe Jeremiah Oyakhilome, ya kai wa mai nakudan agaji, bayan  yin abin da ya kamata, daga karshe wannan mata ta haifi jaririnta lafiya kalau.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post