Kwarto ya yiwa mata da miji dukan tsiya a Kano bayan ya kasa samun biyan bukata

Legit Hausa
Wani magidanci mai suna Mallam Bello da mai dakinsa sun fada wani mummunan hali, yayin da wani mutumi mai suna Sulaiman Saleh ya yankesu da wuka a wuya, hannaye da wasu sassan jikinsu.
Lamarin ya faru ne a ranar Litinin dinnan da ta gabata a kauyen Wutar Kara da ke karamar hukumar Rano ta jihar Kano.
An zargi Sulaiman da kutse a gidan Malam Bello da niyyar afkawa mai dakinsa. Amma sai bai yi nasara ba, saboda matar Mallam Bello ta yi kururuwa wacce ta jawo hankalin mai gidanta ya kawo mata dauki.
Wanda ake zargin ya lura hakarsa ba zata cimma ruwa ba shiyasa yayi amfani da makamin hannunshi don raunata ma’auratan. Ya yanki mijin a wuya da hannayensa inda ita kuma matar ya yanketa a wuya da sassan jikinta.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Kiyawa ya tabbatar da aukuwar wannan lamarin. Ya ce, mutanen anguwar sun kaiwa magidancin dauki don har sun lakadawa wanda ake zargin dukan tsiya.
Magidancin a yayin tattaunawarsa da Freedom rediyo, ya bayyana takaicinsa da matukar alhinin faruwar lamarin
A yanzu dai, ‘yan sanda sun mika wanda ake zargin zuwa asibitin Murtala Mohammed da ke Kano. Sun bazama cigaba da bincike ta bangarensu.
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post