Bayar da bayanan sirri ga masu sace mutane, yansandan jihar Kebbi sun kama mutum 46

Rundunar yansandan jihar Kebbi ta kama masu ba masu sace mutane bayan sirri guda arba'in da shida 46, ta kuma dakile wani yunkurin sace wani mutum domin a karbi fansar Naira Miliyan daya da rabi N1.5m daga wajensa. Kwamishinan yansandan jihar Kebbi Mr. Garba M. Danjuma ne ya shaida wa manema labarai haka a shelkwatan yansanda da ke Birnin kebbi.

Kwamishinan ya ce wani mutum main suna Alhaji Abubakar Chindo wanda ke garin Bunza, a karamar hukumar Bunza ya shaida wa yansanda cewa an kira shi a wayar salula aka bukaci ya biya Naira miliyan daya da rabi ko a sace shi

"Sakamako haka jami'an mu masu bincike suka fara aiki.,wanda ya kai ga kama Muhammed da Abdullahi bisa zargin alaka da wannan yunkuri" inji Kwamishinan yansanda .

Ya kuma kara da cewa rundunarsa ta yi nassarar kama wasu da ake zargi da harkar sace mutane a kananan hukumomin Fakai, Arewa,Danko-Wasagu, Jega, Birnin kebbi, Shanga,, Bunza da Zuru.

Rundunar yansandan ta kuma kama da dama daga cikin masu bayar da bayanan sirri ga masu sace mutane daga karamar hukumar Gwandu , hakazalika ta kama wani mai suna Labbo daga kauyen Ingarje a karamar hukumar Jega, wanda ya ke cikin wani gungun masu sace mutane da suka sace matar Saidu Abdullahi a wannan yanki.

Kwamishina Danjuma ya ce rundunarsa za ta gurfanar da su a gaban Kotu.

.DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post