Yadda Ministan shari'a Abubakar Malami ya sama wa matasa 400 aiki daga jihar KebbiMinistan shari'a kuma babban Joji na Najeriya Alhaji Abubakar Malami ya karbi zayaran wasu shuabanannin matasa da suka yi na'am da manufofi da tsare tsaren ci gaban jama'ar jihar Kebbi gaba daya da Ministan ke yi a fadin jihar Kebbi. Wata kungiyar matasa mai suna Chika Believers Movement ce ta kai masa ziyara a gidansa da ke Birnin kebbi ranar Asabar.

Abubakar Muhammad ABK, babban mai tsare-tsare na kungiyar a jihar Kebbi , Shehu Isah S.Kudu Sakataren kungiyar da sauran manyan manbobin kungiyar na daga cikin wadanda suka gana tare da Minista, saidai shugaban matasa na kungiyar Alhaji Tukur Wasoso bai sami halartar ziyarar ba.

Mujallar ISYAKU.COM ya tattaro cewa Minista Malami, ya samar da guraben aiki ga fiye da mutum dari hudu 400, tun lpkacin da ya zama Minista, kuma makonnin baya ya sama wa matasa goma aikin dansanda a jihar Kebbi.

Haka zalika wakilin mu ya samo cewa, Ministan shari'a Abubakar Malami, ya samar da yanayi na ciyar da musakai da almajirai abinci a gidaje 12, karkashin gidauniyar taimako na Khadi Malami Foundation.


Haka zalika, a kowane karamar hukuma, Ministan ya samar da akalla gida guda daya da ake ciyar da akallam talakawa 100, a Makarantun Almajirai. Harkar tallafi ga masu kananan karfi, taimakawa wajen ilimin al'umma, ingantaccen kiwon lafiya na daga cikin dimbin ayyuka da Minista ke bayar da gudunmuwa ga talakan jihar Kebbi tun kasancewarsa Ministan shari'a.

Abubakar Malami ya ce:

" Na yi magana da shugaban kasa, na bashi shawarar cewa masu harkokin waka, rubuce rubuce, yan Social Media, sun bayar da gagarumar gudunmuwa akan abin da ya danganci mu'amala da ya danganci wannan Gwamnati, kuma sun rike abin da suke yi a matsayin sana'a, suna da hakki kamar kowa na cewa an basu wata kariya. Kuma shugaban kasa ya amince a kan wannan".

" Yanzu haka mun dauki mataki na rijista, horarwa da tsara yadda aikin zai tafi, da tsarin da wadanda abin ya shafa za su iya samun kai ga wannan shirin domin su amfana da wannan shiri na babban Bankin Najeria, Central Bank, kuma horar da mutum 500 zai ci kudi har N15m wanda mun samar da wannan da hadin guiwa tare da Alh. Umaru Dan kane, Faruku Gwandu da sauransu, mun dora wa kanmu haraji na bayar da gudunmuwa, wasu kuma da suka yi alkawari sun bayar da N8m.

" Mun yi wannan ne domin a samar da mutum 500, mu shige masu gaba domin samun biyan bukata Naira miliyan Daya zuwa Naira Miliyan goma domin mu'amala na rayuwa, ko a nan aka tsaya muna da hakki na shige wa mutane gaba tunda Allah ya dora mu a kan wannan. Mun ta'allaka tsarin mu a kan bayar da gudunmuwa ga al'umma tunda Allah ya kaddari hannayenmu na kaiwa inda na sauran jama'a baya kaiwa a Gwamnatance, ya zama wajibi mu taimaka wa al'umma domin su karfafa".
\
Ministan shari'a Abubakar Malami SAN, yana cikin Ministoci da shugaba Muhammadu Buhari ya amince masu a gwamnatinsa, kuma daya daga cikin manyan hadimansa.


DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
 • Previous Post Next Post

  Reported by ISYAKU.COM

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
  https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
  LATSA NAN 

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

  Facebook.com/isyakulabari