Yadda wasu Jaruman Kannywood suka yi auren mutu'a

Daga Legit Hausa Wani sabon rudani ya yi wa masana'antar Kannywood mai kula da shirin fina-finan Hausa dabaibayi, inda aka samu jarum...

Daga Legit Hausa
Wani sabon rudani ya yi wa masana'antar Kannywood mai kula da shirin fina-finan Hausa dabaibayi, inda aka samu jarumi kuma mai shirya fina-finai, Isa I. Isa da kuma jaruma Sadiya Haruna da tona wa junansu asiri.


Isa I. Isa da Sadiya Haruna
Kamar yadda kafar watsa labarai ta freedomradionig.com ta wassafa a shafinta, ta ce wannan rudani ya samo asali ne tun yayin zargin da jaruma Sadiya ta yi a kan jarumi Isa. Jarumar dai ta yi zargin ne gabanin ta kama sunansa inda kuma daga bisani ta bayyana sunansa karara.
Cikin wani faifan bidiyo da jarumar ta saki na kalubalantar jarumin da ya fito ya kare kansa, ta zarge shi da cewa sunyi auren mutu'a, wato dai auren biyan bukata tare da daukewa juna sha'awa na wani tsawon lokaci kayyadadde.
Hakazalika shi ma jarumin ya wallafa wani bidiyo a shafinsa na zauren sada zumunta, inda labartawa duniya cewa ya aikata wasu ababe na rashin kyautawa da kuma rashin daidai tare da neman gafarar al'umma da masoyansa.
Freedom Radio Nigeria ta tattaro cewa, jarumin daga bisani ya goge wannan bidiyo, amma dai tuni aikin gama ya gama domin kuwa fasahar zamani ta sanya bidiyon ya yi duk wani shawagi da zai yi a dandalin YouTube.
A wani lokaci da ya gabace mu, jarumi Isa I. Isa cikin wani bidiyo yayin amsa tambayar menene ainihin alakarsa da jaruma Sadiya Haruna, ya ce ba komai bane face ta kasance matarsa.
Sa'o'i uku bayan faruwan hakan, ita ma kuma jaruma Sadiya ta wallafa wani sako a shafinta na Instagram da cewa Isa ya taba debo mata 'yan sanda har gida.
Daya daga cikin jaruman dandalin Kannywood wadda ita ma ta yi kaurin suna a zaurukan sada zumunta, Muneerat Abdussalam, ta bayyana mamakin yadda rikici ya barke a tsakanin jaruman biyu, inda ta bayyana Isa da kuma Sadiya a matsayin masoya biyu da suka taba kai mata ziyara.
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
IDAN KA GAN WANI ABU NA FARUWA, HANZARTAB KA SANAR DA MU A ISYAKULABARI@GMAIL.COM
Name

'YANSANDA,1,AL-AJABI,22,AREWA,45,BIDIYO,147,BINCIKE,1,BIRNIN-KEBBI,375,BOLLYWOOD,2,BUHARI,10,DUNIYA,110,ENGLISH,27,FADAKARWA,126,FASAHA,14,FITACCEN LABARI,19,HOTO,175,HOTUNA,90,JAKAR MAGORI,1,LABARI,2981,NISHADI,282,OSCAR,2,Samaila Yombe,42,SANARWA,31,SHARHI,16,SIYASA,387,TARIHI,11,TSARO,354,WASANNI,18,
ltr
item
ISYAKU.COM: Yadda wasu Jaruman Kannywood suka yi auren mutu'a
Yadda wasu Jaruman Kannywood suka yi auren mutu'a
https://1.bp.blogspot.com/-6IjvbzKEJKU/XaNNbTF-ojI/AAAAAAAAXZ8/6wi3h6o7Mz4dd0CByIXybX2CvbLlDP6RQCLcBGAsYHQ/s320/0d755452b65da889.jpg
https://1.bp.blogspot.com/-6IjvbzKEJKU/XaNNbTF-ojI/AAAAAAAAXZ8/6wi3h6o7Mz4dd0CByIXybX2CvbLlDP6RQCLcBGAsYHQ/s72-c/0d755452b65da889.jpg
ISYAKU.COM
https://www.isyaku.com/2019/10/yadda-wasu-jaruman-kannywood-suka-yi.html
https://www.isyaku.com/
https://www.isyaku.com/
https://www.isyaku.com/2019/10/yadda-wasu-jaruman-kannywood-suka-yi.html
true
3052478943858316060
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS CONTENT IS PREMIUM Please share to unlock Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy