Sarki Sanusi ya tube rawanin wani babban basarake a fadarsa

Legit Hausa
Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II yayi umurnin sallaman Maja Siddin Sarkin Kano, Alhaji Auwalu akan shiga sahun masu bikin maraba da Gwamna Abdullahi Ganduje a ranar Laraba da ya gabata.
An kuma bukaci Maja Sidden Sarkin Kano, wanda ke kula da kawata dokin Sarkin, da ya tashi daga gidansa wanda ya shafe shekara 30 a ciki.
Jaridar The Nation ta rahoto cewa lamarin ya haifar da tashin hankali sosai a majalisar sarkin Kano.
Alhaji Auwalu ya fara shiga matsala ne lokacin da ya daga hoton marigayi sarkin Kano, Mai martaba, Sarki Ado Abdullahi Bayero domin taya Ganduje murna yayinda dogon ayarin motocin gwamnan suke wucewa ta fadar sarki daga filin jirgin sama na Kano zuwa gidan gwamnati a ranar Laraba da ya gabata.
Wata majiya ta fadar sarki wacce ta nemi a boye sunan ta, tace abunda Auwalu yayi ya matukar bata ran sarki Sanusi wanda baya a Kano a lokacin dawowar Ganduje.
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post