Wata mata da yaranta 3 sun mutu bayan gini ya fada masu lokacin ruwan sama

Wata mata mai suna  Mrs. Jumiah Utache, tare da yayanta guda uku masu suna Faith yar shekara 9, da Domino mai shekara 2 tare da Daniel mai shekara 1, sun mutu bayan sashen wani gidan sama da ke kusa da gidansu ya rushe ya fado ma gidansu yayinda suke cikin gidan sa'ilin da ake sheka ruwan sama, lamari da ya yi sanadin mutuwansu nan take a unguwar Magodo a birnin Lagos ranar Asabar.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru a gida mai lamba 48 da ke unguwar Orisa, sashe na 1 unguwar Magodo na birnin Lagos.

Sai dai  wata majiya ta ce maigidan matan kuma uban yaran da suka mutu Emmanuel Utache, bai mutu ba, amma ya sami raunuka.

DAGA ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp

https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post