Yadda satan awaki ke addaban mutane a Nassarawa2 Birnin kebbi

Satan awaki da bunsuru a garin Birnin kebbi na neman ya zama ruwan dare a tsakanin al'umma ganin yadda awaki ke batan dabo cikin dare kafin bullowan Alfijir, musamman a unguwar Nassarawa 2 da kewaye.

Mafi yawan lokaci masu wadannan dabbobi sukan barsu ne su yi kiwo ko da a cikin dare, ganin yadda halin awaki yake a wajen kiwo. Sakamakon haka ake zargin cewa awakin kan yi wa jama'a barna wasu lokuta.

Saidai wata majiya ta labarta mana cewa ana zargin cewa wasu bata gari ne ke yawatawa cikin dare a mota, kuma suke sace wadannan dabbobi sai su saka a mota su arce.

Amma bincike da Mujallar isyaku.com ta gudanar ya nuna cewa mafi yawan wadanda ake sace wa awakin sukan bar wa Allah ne marmakin su kai rahotu wajen hukumomi.

Wata mata mai kiwon awaki ta ce " Wannan ne karo na hudu da aka sace mani akuya, kumma wanda aka sace kwana uku da suka wuce, tana dauke da juna biyu. Duk mai yi mana wannan aiki Allah ka tona asirinsa ko a ina yake kuma Allah ka saka mana".

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post