Yadda hukuncin Kotuna ya kasance tsakanin Gwamnatin jihar Kebbi,DSS da Aisha Zakari

Wata babban Kotun taraayya da ke garin Birnin Kebbi ranar Talata 29/10/2019, ta yi watsi da karar da babban Lauya mai kare hakkin bil'adama a jihar Kebbi ya shigar a gabanta wanda ya nemi Kotun ta sa Gwamnatin jihar Kebbi da hukumar DSS su biya Nasiru Jatau tare da matarsa Aisha Zakari diyyan Naira Miliyan dari biyar N500m, da ban hakuri bisa kamasu tare da tsarewa har kwana 13 ba tare da an gurfanar da su a gaban Kotu ba.

Kalli jawabi daga Layan A,A Fingilla:.Haka zalika, wata Kotun Majistare a garin na Birnin Kebbi ranar Talata, ta daga shari'ar da hukumar DSS ta gurfanar da Aisha Zakari a gabanta bisa tuhumar tayar wa Gwamnan jihar Kebbi hankali ta sakon TEXT a wayar salula har illa masha Allahu.

Kalli dalili daga Lauya A.A. Fingilla:Mijin Aisha Zakari, watau Alhaji Nasiru Jatau ya yi jawabi mai ratsa jiki kan hukuncin babban Kotun tarayya na yin watsi da karar da suka shigar.

Kalli jawabin Nasiru Jatau:Mujallar isyaku.com na yi maku godiya da kasancewa tare da mu har zuwa wannan lokaci. Muna fatan kun gamsu da rahotannin da muka kawo maku a wannan lamari, tare da fatan Allah ya kiyaye mu gaba daya daga kaddarorin rayuwa. Mun gode.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
 • Previous Post Next Post

  Reported by ISYAKU.COM

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
  https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
  LATSA NAN 

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

  Facebook.com/isyakulabari