Kotu ta sake daga shari'ar tsohon Gwamnan jihar Kebbi Sa'idu Dakingari

Wata babban Kotun tarayya da ke garin Birnin kebbi ranar Litinin, ta ci gaba da sauraron shari'ar da hukumar EFCC ta gurfanar da tsohon Gwamnan jihar Kebbi Alhaji Sa'idu Nasamu Dakingari tare da wasu mutum biyu bisa zargin aikata ba daidai ba da wasu kudade a lokacin zaben 2015. 

Ana zargin tsohon Gwamnan ne da aikata ba daidai ba dangane da wasu makuddan kudade da ake zargin cewa an fitar aka raba tsakanin wasu yan siyasa.


Dakingari tare da wasu mutum biyu, sun bayyana a akwatin wadanda ake tuhuma a Kotun, yayin da ake gudanar da shari'ar.

Alkalin Kotun ya daga shari'ar har zuwa ranar 11 ga watan Disamba na 2019, domin ci gaba da shari'a.

Bayan fitowa daga Kotun, wakilin Mujallar isyaku.com ya lura cewa, Dakingari tare da wadanda ake tuhuma suna cikin yanayi da ke nuna kwanciyar hankali, sanye da babban riga da tabarau, Dakingari ya gaisa da wasu ma'aikatan Kotun yayin da ya fito kafin ya shiga motarsa tare da Lauyoyinsa suka fice daga harabar Kotun.

Jama'a da dama, suna yaba wa tsohon Gwamnan, sakamakon alakanta shi da ayyuka masu yawa da amfani ga talakawa da ya yi a jihar Kebbi, kusan a kowane lungu na jihar, musamman a Karkara.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
 • Previous Post Next Post

  Reported by ISYAKU.COM

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
  https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
  LATSA NAN 

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

  Facebook.com/isyakulabari