Wata daliba ta tona asirin wani Lakcara da ya nemi ya yi lalata da ita, ga yadda hirarsu ta kasanceLegit Hausa

Bayan bayyanar tonon sililin da ake yiwa malaman jami'a akan lalata da suke yi da dalibai su ba su maki, wata budurwa mai suna Busayo ta bayyana yadda tayi fama da wani dan iskan malamin jami'a.

A cewar ta Lakcaran wanda ta bayyana sunansa da Dr. Abdul ya fadar da ita jarrabawar shi saboda ta ki yarda ta yi lalata da shi.

Budurwar ta kuma wallafa hotunan hirar da suka yi da shi a manhajar WhatsApp domin tabbatar da faruwar lamarin.

A hotunan da ta wallafa na hirar ta su a WhatsApp din, malamin yana ta faman rokon ta gafara amma ita kuma ta yi kunnen uwar shegu da shi.

A hirar ta su Busayo ta yi ta zagin Lakcaran, hakan na nuni da cewa har yanzu ta na jin haushin irin abinda Dr. Abdul ya yi mata. Ga dai hotunan da Busayo ta wallafa na hirar da suka yi da Malamin Jami'ar a kasa:DAGA ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp

https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post