Gwamna Bagudu ya kasa ganawa da kungiyar tsofaffin jami'an DSS wata 19 bayan sun nemi haka

Wata goma sha tara (19) bayan kungiyar tsofaffin jami'an tsaro na hukumar tsaro na Department of State Services DSS, watau Association of Retired Officers of Department of State Services Of Nigeria ARODSSON, reshen jihar Kebbi ta nemi ta gana ta hanyar ziyara ga Gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu tun mako na karshen watan Maris (March) 2018, amma lamarin ya gagara har zuwa yau.

Wani bincike da Mujallar isyaku.com ya gudanar kan wannan lamari, ya tabbatar cewa sashen Protocol na gidan Gwamnati sun yi aikinsu kamar yadda ya kamata, sun karbi takarda, har takarda ta kai wajen Gwamna Bagudu, wanda ya albarkaci takardar da cewa a nemi rana mafi dacewa a sa domin jami'an hukumar su gana tare da shi ( Find suitable date).

Wannan ya sa shugabannin kungiyar suka nemi sashen Protocol na gidan Gwamnati su sanar da su akalla kwana biyu idan har Gwamna ya bukaci ganinsu, domin su sanar da sauran manbobin kungiyar da ke nesa kamar Yauri, Zuru da sauransu.

Amma tun wancan lokaci, har yau an kasa yin gaba da wannan zance. Saidai wani tsohon jami'an wannan hukumar ya ce " Wannan lamari da daure kai, wannan Gwamna ya gana da kungiyoyi da dama, na masu sayar da kifi, tumatur, da sauran kungiyoyi, amma kuma aka yi biris da namu bukata. Bai san abin da muke dauke da shi ba, kuma ziyarar mu ai domin ci gaban jihar mu ne. Dukkan mu yan asalin jihar Kebbi ne".

Bincike ya nuna cewa, kungiyar tsofaffin jami'an tsaro na DSS reshen jihar Kebbi, tana da manyan hafsoshi wadanda suka yi ritaya da darajar mukami na Manjo janar a gidan soja har fiye da mutum hudu, bayan wasu masu  darajan mukamin Kwamishinan yansanda da mataimakansu.

Hakazalika binciken ya fayyace cewa shugaban hukumar tsaro na DSS da ke kowane jiha, kai tsaye shi ne ke rike da mukamin babban uban kungiya (Patron).To amma wane rawa ne Daraktan hukumar tsaro na DSS na jihar Kebbi a yanzu M.M Kaumi ya taka wajen ganin cewa kungiyar ta sami zantawa da Gwamna Bagudu, ganin cewa shi ne uban wannan kungiya kamar yadda yake a tsare daga babban shelkwatan hukumar na kasa?.

Bayanai sun nuna cewa, Gwamnan jihar Borno ya nada dan wannan kungiya na tsofaffin jami'an DSS a matsayin mai bashi shawara a kan harkar tsaro, haka Gwamnan jihar Benue da sauran jihohi da suka mutunta kuma suka martaba manbobin wannan kungiyar jami'an tsaro mafi kishin kasa da tsare gaskiya a tarihin ayyukan tsaro na Najeriya.

Mujallar isyaku.com ya samo cewa a zamanin tsohon Daraktan hukumar DSS na jihar Kebbi a zamanin Gwamna Sa'idu Dakingari, watau Alhaji Ibrahim Katsina, shi da kansa ne ya jagoranci yan kungiyar kuma suka gana da Sa'idu Dakingari, haka kuma sauran Daraktocin hukumar da suka gabata.

Daga karshe, wa ke da alhaki a kan wannan lamari ?.

DAGA ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp

https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
 • Previous Post Next Post

  Reported by ISYAKU.COM

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
  https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
  LATSA NAN 

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

  Facebook.com/isyakulabari