Wani mutum mai 'ya'ya 100 ya auro mata 4 don bukatar karin haihuwa

Legit Hausa
Wani mutum dan kasar Uganda mai yara 100 ya karo mata hudu sakamakon Karin bukatar haihuwa da yake.
Nulu Ssemakula mai shekaru 94 a duniya mazaunin kauyen Ruyonza ya kara fadada iyalansa.
Ssemakula musulmi ne wanda ya sake farali a shekara 1977 kamar yadda jaridar Ugandan Monitor ta ruwaito.
Ssemakula wanda ya yi nasarar fadad iyalinsa na da mata sama da 19 wadanda suka Haifa masa yara 100 kuma a halin yanzu yana bukatar kari. Karamin dansa yana da watannni 10 a duniya kuma amaryarasa mai shekaru 24 na da cikin wani dan.
A halin yanzu yana tare da ‘ya’yansa 66 kanana. A yayin da awasu daga cikin yaransa suka haifa masa jikoki, kakan y ace shi kuwa yana bukatar Karin haihuwa, a don haka ne ya karo mata 4.
Ssemakula ya auri matarsa ta farko ne a shekarar 1952 wacce bata dade bay a karo mata abokan zama 5.
“Matana 4 suka rasu a gidana, wasu kuma da suka nuna bazasu iya zama dani ba sun tafi sun barani da yara. Zan kuma kara auro wasu matan in har ina da sauran kwana. A wajen mata da yarana nake samun nishadi. Su ne gaskiyar arzikina.” in ji Ssemakula.
A halin yanzu, Ssemakula ya gina masallaci da makarantar firamare da kuma in jin tatsar nonon shanu don kula da iyalinsa.
DAGA ISYAKU.COM

Previous Post Next Post