Boko Haram sun kashe sojoji 847 a Borno - Ndume

Legit Hausa
Shugaban kwamitin majalisar dattawa akan sojin kasan Najeriya, Sanata Ali Ndume, ya ce kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram, ta salwantar da rayukan dakarun soji 847 daga shekarar 2013 kawo wa yanzu.
Jaridar The Nation ta ambato Sanatan yana cewa, an binne gawarwakin sojojin da suka riga mu gidan gaskiya a wata makabartar dakarun soji da ke birnin Maidugurin jihar Borno.
Sai dai Sanatan ya ce wannan adadi bai hadar da na sojojin da mayakan Boko Haram suka hallaka ba kuma aka binne su a wasu makarbartun dakarun sojin na daban.
Furucin Sanata Ndume ya zo ne a yayin da mambobin kwamitin da yake jagoranta suka ziyarci jihar Borno.
Nduma ya ce binciken da kwamitinsa ya gudanar ya gano cewa sojoji da ke filin daga wajen tunkarar mayakan Boko Haram ba su da wadatattun kayan yaki kuma wadanda suka mallaka suna da nakasun nagarta.
Hakazalika Sanatan ya ce adadin sojojin da ke tunkarar ta'addanci a yankin Arewa maso Gabashin ya yi karancin gaske, lamarin da ya ke kiran gwamnatin Najeriya a kan aike wa da wasu dakarun domin an ce hannu da yawa maganin kazamar miya.
Ya kara da cewa, kwamitinsa na ci gaba a gudanar da bincike kan zargin wasu kungiyoyi masu zaman kansu da taimako da kuma goyon bayan mayakan Boko Haram.
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post