Rundunar soji ta kallubalanci Ndume kan ikirarin kisan sojoji 847

Legit Hausa
Rundunar Sojojin Najeriya ta bukaci Sanata Ali Ndume sa kwamitin majalisa kan sojoji da su gabatar da hujojjin su da ke nuna cewa 'yan ta'addan kungiyar Boko Haram sun kashe sojojin Najeriya fiye da 840.
Sanatan mai wakiltan Borno ta Kudu ya ce a ranar Talata cewa daga 2013 zuwa yanzu a kalla sojoji 840 ne aka birne a makabartar sojoji da ke Maiduguri babban birnin jihar Borno.
Amma mai magana da yawun rundunar sojojin Najeriya, Sagir Musa ya karyata ikirarin na Ndume.
A hirar wayar tarho da The Cable tayi da Sagir, ya ce, "Idan abinda ya ce kenan sai ya gabatar da hujojji. Ina ya samo wadannan bayanin? Ya bayyana mana."
A wata rahoton da Wall Street Journal ta wallafa a watan Augusta, ta ce fiye da sojojin Najeriya 1,000 ne da aka kashe a fagen fama aka birne cikin sirri a Maiduguri.
A rahoton ta da ce ta samu daga wata majiya daga sojoji, Wall Street Journal din ta ce adadin sojojin da aka yi wa irin wannan birnewa zai iya dara hakan.
A cikin watanni da suka gabata, 'yan ta'addan sun kai hare-hare da sansanin sojoji da wasu garuruwa a Borno inda suka kashe wasu sojojin.
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post