Tsofaffin jaruman Kannywood mata guda 15 da suka dawo harkar fim bayan mutuwar auren su


Legit Hausa

Kamar yadda muka ruwaito muku a rahoton dawowar jaruma Farida Jalal harkar fim, cewa yanzu kamar yayi ne ake na dawowar tsofaffin matan da suka taka rawa a masana'antar Kannywood, hakan yasa muka bincika muka zakulo muku wasu daga cikin jaruman Kannywood mata da suka taka rawar gani a baya a masana'antar ta Kannywood kana kuma bayan mutuwar auren su suka dawo harkar.

Koda yake wasu bamu da tabbacin sun dawo fim din ka'in da na'in kasancewar bamu gansu cikin fim ba amma akan gansu jefi-jefi cikin 'yan fim din, amma kuma da yawan su sun tabbatar da dawowar su inda wasu suka bayyana da bakin su wasu kuma kawai sai ganin su aka cigaba da yi a cikin fim.

Ga dai jerin jaruman a kasa:

1. Hadiza Kabara
2. Hafsat Shehu
3. Fati Muhammad
4. Maijidda Abbas
5. Fati Baffa Fage
6. Farida Jalal
7. Rukayya Dawaiya
8. Saima Muhammad
9. Samira Ahmad
10. Fauziyya Mai Kyau
11. Sadiya Gyale
12. Sadiya Kabala
13. Maryam Ab Yola
14. Tumba Gwaska
15. Fati KK

Maryam Ab Yola, Sadiya Kabala da Tumba Gwaska ba za a kira su da tsofaffin jarumai ba kasancewar ba wacce ta shekara goma a masana'antar a cikin su sai dai sun shiga wannan lissafi ne saboda sun yi aure kuma sun fito sun cigaba da harkar. Haka zalika ba wai ana nufin wadannan sune kawai jaruman Kannywood mata da su yi aure suka fito ba amma sune ake kyautata zaton sun dawo harkar fim, kuma ana ganin su ne a cikin dukkan sha'ani na 'yan fim.
 

DAGA ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp

https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN