Gwamnati ta bai wa malamai 30 kwangilar addu'a a Saudiyya. Karanta dalili

Legit Hausa
Farfesa Babagana Zulum, gwamnan jihar Borno, ya bai wa wasu malamai kimanin 30 mazauna birnin Makkah na kasar Saudiya, kwangilar gudanar da addu'o'i da kuma dawafi domin rokon Mai Duka ya magance musibar kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram.
Cikin wata sanarwa da ta fito daga bakin mai magana da yawun gwamnan, Isa Gusau, ya ce gwamnatin Borno ta bai wa wadannan malamai 30 mazauna birnin Makkah kwangilar gudanar da addu'o'i wajen rokon 'Buwayi Gagara Misali' da ya wanzar da aminci a jihar da kuma kasa baki daya.
A cewar Alhaji Gusau, gwamna Zulum ya kulla wannanjarjejeniya da zababbun mutanen 30 mazauna birnin Makkah, domin su dawwama wajen gudanar da addu'o'i da kuma dawafi wato zagayen Ka'aba wajen rokon Mai Kowa Mai Komai da ya saukar da aminci a jihar Borno da kuma kasar nan.
Ya ce malaman 30 da aka bai wa wannan kwangila sun fito ne daga jihohin Borno, Katsina, Zamfara, Kano da kuma wasu sassa na yankin Arewa maso Gabas, da suka shafe fiye da shekaru 10 na zama a kasar Saudiya.
Cikin wadanda gwamnatin jihar Bornon ta kulla yarjejeniyar da su sun hadar da wani dattijo da ya shafe kimanin shekaru 40 a farfajiyar masallaci mai alfarma na Ka'aba wajen gudanar da ibada.
Jaridar The Punch ta ruwaito kakakin gwamnan yana cewa, an kulla yarjejeniyar tare da malaman 30 yayin da gwamna Zulum ya gana da su a ranar Juma'ar da ta gabata cikin birnin Makkah.
Alkalumma sun tabbatar a cewa ya zuwa ya yanzu kungiyar masu tayar da kaya baya ta Boko Haram ta haura kimanin shekaru da daura damarar ta'addanci a kasar nan musamman yankin Arewa maso Yamma da kuma wasu kasashen da ke makwabtaka da Najeriya.
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN