Tallafin N30m ga Kiristocin Zuru, Janar Bamayi ya warware wani zance

Janar Ishaya Bamayi mai murabus, tsohon shugaban rundunar askarawan sojin kasa na Najeriya a zamanin tsohon shugaban kasa na mulkin soji, Janar Sani Abacha, ya ce gudunmuwar Naira miliyan talatin da Gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu ya ba Kiristocin kasar Zuru abin yabawa ne, amma ya bukaci kada a mayar da abin zuwa lamarin siyasa.

Janar Ishaya Bamayi ya ce " Ban ce kada Gwamna ya taimaka wa addini ko wasu kungiyoyi ba, dukkanmu muna karkashin shi ne, domin addini sha'ani ne tsakanin mutum da Allah, amma kada a hada zancen addini da siyasa. Ni Kirista ne amma yayata ni na fara kaita Makka a 1979 tun lokacin da nike da mukamin Manjo a gidan soja, kuma na kai fiye da mutane 40 Makka, domin in nuna maka cewa na wuce matsayin cewa in zauna kan addini ko siyasa domin lamari da ya shafi ci gaban kasar Zuru. Hakazalika, na bayar da tallafi da dama domin gina Masallatai, Wannan na yi ne tsakani na da Allah ba wai domin siyasa ba".

Janar Bamayi ya kara da cewa " Na yi magana da shugaban kungiyar kiristoci na Najeriya reshen  Zuru Rev. Manga, tare da Ambassada Yakubu Kwari da sauransu. Na gaya masu cewa taimakawa addini daidai ne, amma kada a mayar da abin ya zama lamarin siyasa"

."Na ji cewa Gwamna ya ce a yi amfani da N16m a kammala ginin wani Mujami'a watau Chochi a Zuru, ragowan N14m a raba wa sauran Mujami'u a kasar Zuru".inji Bamayi.

"Zancen cewa Gwamna Bagudu ne ya fara taimakawa Kiristocin Zuru, wannan ba gaskiya bane, domin tsohon Gwamna Sa'du Dakingari ya gina mana Sakatariyar Mujami'ar UMCA daga farko har karshe ba tare da an mayar da lamarin na siyasa ba. Kuma yanzu haka nan ne Shugaban kungiyar Kiristoci na Najeriya  CAN reshen Zuru, tare da sauran maikatansa da Supiritanda na Mujami'un Zuru suna amfani da wannan Sakatariya da Dakingari ne ya gina mana yanzu haka, kuma ba tare da an mayar da lamarin na siyasa ba har ya bar mulki".

Janar Ishaya Bamayi, wanda yaya ne ga marigayi Janar musa Bamayi, yana daya daga cikin manyan Dattijai na kasar Zuru wanda tarihi ba zai taba mantawa da shi ba a jihar Kebbi da Masarautar Zuru.. Janar Ishaya ya dauki dubban samari da matasan kasar Zuru da jihar Kebbi a cikin aikin soji, kuma bayanai sun ce yana daya daga cikin wadanda suka taimaka aka sami jihar Kebbi a zamanin mulkin soja.

DAGA ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp

https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post