• Labaran yau


  Shugaba Buhari ya nada wa Aisha sabbin hadimai 6, duba sunayensu

  Legit Hausa
  Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin sabbin hadimai na First Lady ta Najeriya, Aisha Buhari kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
  Sanarwar da Direktan watsa labarai na First Lady, Sulaiman Haruna ya fitar ya ce wadanda aka nada sun hada da:
  1. Dakta Mairo Almakura - Mai taimakawa ta musamman kan African First Ladies Mission (AFLPM)
  2. Muhammad Albishir - Mai taimakawa na musamman kan Kungiyar Cigaba da First Ladies na kasashen Afirka (OAFLD).
  3. Wole Aboderin - Mai taimakawa na musamman kan kungiyoyin masu zaman kansu (NGOs)
  4. Barrista Aliyu Abdullahi - Mai taimakawa ta musamman kan Kafafen watsa labarai
  5. Zainab Kazeem - Mai taimakawa ta musamman kan Harkokin cikin gida da taruka.
  6. Funke Adesiyan - Mai taimakawa ta kusa Harkoki cikin gida da taruka
  Dukkan wadanda aka nada za su fara aiki nan take.
  DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Shugaba Buhari ya nada wa Aisha sabbin hadimai 6, duba sunayensu Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama