Yan sanda sun gurfanar da mutumin da ya kashe Mata 10

Legit Hausa
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta gurfanar da wani mutum mai suna Gracious David-West bayan ya amsa cewar ya kashe Mata 10 kamar yadda ake zarginsa da aikata wa.
Da yake magana a gaban alkalin kotun da aka gurfanar da shi bayan an gurfanar da shi, David-West ya ce, "mai girma mai Shari'a, na kashe mata guda 9 a Otal, sai wata guda daya, cikon ta 10, wacce ban samu ikon kashe ta ba, amma na daure ta a jikin kujera."
Sai dai, ya nemi afuwa bayan ya amsa laifuka 9 daga cikin 10 da ake tuhumarsa da aikata wa tare da bayyana cewa ya aikata laifukan ne bisa rudin shaidan.
David-West ya bukaci kotun ta umarci rundunar 'yan sanda ta mayar masa da kudinsa N60,000, sarka da agogonsa da suka kwace a hannunsa.
Yanzu haka gwamnatin jihar Ribas, a karkashin ofishin kwamishinan Shari'ar, Zacchaeus Adango, ta karbi ragamar cigaba da Shari'a tuhumar David-West.
Alkalin kotun, Jastis Enebeli, ya amince da bukatar gwamnatin jihar tare da lasar takobin ganin ba a samu tsaiko a Shari'ar ba kafin daga bisani ya daga sauraron Shari'ar zuwa ranakun 18, 21, 27 da 29 ga Nuwamba, yayin da za a cigaba da tsare David-West a gidan yari.
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post