An bankado wani gidan da 'yan mata masu kananan shekaru ke haihuwa don safarar jariran

Legit Hausa
Yan sandan na sashin binciken manyan laifuka na tarayya (FCIID) sun gano wani gidan karuwai inda aka tara 'yan mata masu kananan shekaru ana yin lalata da su don a sayar da jariran idan sun haihu.
An gano wurin mai suna Dafog Hotel a Shimawa wani gari da ke nan iyakan Legas da Ogun ne a safiyar ranar Laraba inda aka kama maza biyu da mata 14.
Wadanda aka kama sun hada da mai otel din, Gbenga Olayinka, dan uwansa Adekunle Oshineye, wasu karuwai uku - Happiness Daniel, Favour Nkume da Glory Ewelike tare da kuma kananan yara tara.
Kananan 'yan matan sun bayar da sunayensu kamar haka Chisom Onyekwere, Chinonso Okoro, Stella Emmanuel, Gift Wada, Chidinma Emmanuel, Tracy Favour, Success Onu, Comfort Francis, Njoku Divine, Destiny Chibuike da Amanda Chima.
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post