Jami’an Road Safety sun kashe mutumin daya hanasu cin hanci, sun boye gawarsa


Legit Hausa

Wasu baragurbin jami’an hukumar kare haddura ta kasa, FRSC, dake aiki a ofishinsu na Abudu jahar Edo sun kashe wani bawan Allah mai suna Odion Samuel sa’annan suka binneshi cikin wani kabari mara zurfi, inji rahoton jaridar Sahara Reporters.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito sunayen jami’an da suka aikata wannan aika aika kamar haka, Francis Igoh, Sunday Ogi, Samson Alolade da kuma Joseph Onolade, kuma sun kashe Odion ne saboda ya hanasu karbar cin hanci da rashawa daga hannun wani direba.

Wannan mummunan lamari ya auku ne a ranar 14 ga watan Oktoba a kusa da tsaunin Okhuaihe dake kan babbar hanyar Bini zuwa Agbor, inda da fara jami’an suka fara tsare motar tare da tuhumar direban motar da sacewa da kuma yin garkuwa da Odion.

Sai dai daga bisani binciken Yansanda ya nuna cewa jami’an FRSC ne suka kashe Odion, bayan sun sha dan karan tambaya daga wajen Yansanda sai suka garzaya da Yansanda zuwa inda suka binne gawar mamacin.

Kaakakin Yansandan jahar Edo, DSP Chidi Nwabuzor ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya bayyana lamarin a matsayin laifin kisan kai da gangan, sa’annan yace zasu gurfanar da mutanen biyu gaban kotu da zarar sun kammala gudanar da bincike.
 

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post