Kungiyar kwadago tace bata aminta da N30,000 ba a matsayin sabon karancin albashi

Legit Hausa
A ranar Litinin da ta gabata ne, ma'akatan gwanati a jihar Legas, sun ce ba zasu karbi kasa da N50,000 ba a matsayin karancin albashi.
Kamar yadda shugaban kungiyar kwadago na jihar, Funmi Sessi ta sanar, ta ce suna bukatar sake sabon ciniki gani da 'yadda Legas take'.
Ta jaddada cewa, ma'aikatan jihar Legas na fuskantar wahalhalu da yawa kafin su kai wajen aiki, don haka bazasu aminta da N30,000 ba a matsayin karancin albashin.
Sessi tace, ba a biyan ma'aikatan yadda ya dace, wanda hakan ne ke kawo karin tabarbarewar lamurra.
Ta kara da cewa, sabuwar bukatar ma'aikatan ta biyo bayan bukatarsu ne yayin bikin ranar halastattun aiyuka na duniya, wanda ake yi duk ranar 7 ga watan Oktoba a fadin duniya.
Ta ce: "Dalili shine, Legas gari ne na musamman. Sufuri da kudin haya da hadurran da ke kan tituna ba daya yake da sauran garuruwa ba. Zuwa aiki ko kasuwa a nan, ba daya yake da jihar Ogun ba,"
"Bukatar mu itace, bayan an biya karancin albashi a N50,000 kuma muna so akalla a biya karamin ma'aikaci N15,000 alawus din hadurra." in ji ta.
Ta ce, "Lokacin da 'yan majalisar dattawa da na wakilai ke amsar miliyoyi, kunji wani labari? Amma biyan N30,000 a matsayin karancin albashi ya dau shekaru 2 ana ciniki."
Daily Nigerian ta ruwaito cewa, ma'aikatan sun yi tattaki a manyan titunan Legasa zuwa sakateriyar Alausa.
Ma'aikatan sun taru a gaban majalisar jihar Legas bayan tattakin lumanar da suka yi daga Ikeja kasan gada.
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Previous Post Next Post